26 Yuli 2025 - 23:04
Source: ABNA24
Iran: 'Yan Ta'adda Sun Kai Hari A Ginin Shari'a A Zahedan Mutane 6 Sun Yi Shahada 22 Sun JIkkata

Wasu ‘yan ta’adda da ke dauke da makamai sun kai farmaki kan ginin shari’a da ke kan titin Hurriya a cikin birnin Zahedan, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi da kutsa kai cikin ginin, lamarin da ya haifar da rudani da kawo daukin jami’an tsaro a yankin.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbayt (AS) - ABNA – ya habarta cewa:  a safiyar yau Asabar ne wasu ‘yan bindiga da ke da alaka da kungiyar ta’addanci ta “Jaish al-Zulm” suka kai wa ginin shari’a hari a birnin Zahedan. a wani sabon lamari da ya shafi daya daga cikin muhimman cibiyoyin shari'a a lardin Sistan da Baluchestan.

Wasu ‘yan ta’adda da ke dauke da makamai sun kai farmaki kan ginin shari’a da ke kan titin Hurriya a cikin garin Zahedan, inda suka bude wuta da shiga ginin, lamarin da ya haifar da rudani da kuma kawo daukin jami’an tsaro a yankin.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyar hasarar rayuka da kuma asarar dukiyoyi da har yanzu ba a bayyana ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan irin barnar da aka yi.

Kungiyar 'Yan Ta'adda "Jaishuz-Zulm" Ta Dauki Alhakin Wannan Harin Na Ta'addanci.

Bayan kai harin, jami’an tsaro da na jami’an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa, inda suka kafa tsauraran matakan tsaro a yankin, sannan suka fara kai dauki tare da zakulo maharan tare da cafke su.

An fitar da wasu da dama daga cikin wadanda suka samu raunuka daga ginin shari'a tare da taimakon jami'an ceto tare da kai su cibiyoyin lafiya ta motar daukar marasa lafiya. Jama’a da ma’aikatan shari’a kuma sun bar wurin tare da taimakon jami’an tsaro.

Cibiyar yada labarai ta ma’aikatar shari’a ta sanar da cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a ma’aikatar shari’a a lardin Sistan da Baluchestan da safiyar yau. Bisa binciken da aka yi, an kawo karshen yanayin tashin hankalin da aka haifar a ginin ma’aikatar shari’a. Mutane da dama ne suka jikkata a wannan ta'addancin, kuma jami'an agajin gaggawa na nan a wurin.

Your Comment

You are replying to: .
captcha